in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardar MDD ya bukaci hadin kai wajen fuskantar sauyin yanayi a yankin Sahel na Afirka
2013-11-08 10:18:38 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon a ranar Alhamis din nan 7 ga wata, a lokacin ganawarsa da shugaban kasar Burkina Faso Blaise Campaore, ya bukaci karin hadin kai wajen fuskanatar sauyin yanayi a yankin Sahel na Afrika.

A yayin wannan ziyarar tare da shugaban bankin duniya Jim Yong Kim da sauran manyan jami'an hukumomin raya kasa, Mr. Ban ya gana da shugaba Campaore, inda suka tattauna kokarin yankuna wajen fuskantar matsalar tsaro, jin kai da barazanar samun cigaba, in ji mataimakin kakakin magatakardar Farhan Haq a ganawarsa da manema labarai.

Mr. Ban ya ce, duk da kokarin da kasar ta Burkina Faso ke yi wajen inganta zaman lafiya da tsaro a yankin Sahel, kasar na daya daga cikin kasashen da sauyin yanayin ya fi tsanani, don haka akwai bukatar kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta kara kaimi don taimaka mata rage wannan matsala.

Shugaban na MDD ya kuma jaddada goyon bayan majalissar ga al'ummar yankin na Sahel, yankin da yake a tsakanin hamadan Sahara daga arewa da kuma yankin Savanna na kasar Sudan daga kudu.

Burkina Faso dai ita ce kasa ta uku cikin kasashen da shugaban MDD ke ziyarta wanda ya riga ya je Mali, da Niger, daga nan sai kasar Chadi da zai zama zangon karshe a cikin ziyarar tasa.

Wannan shi ne karo na biyu da shugabannin MDD da na bankin duniya suka ziyarci Afrika a cikin watanni 6. Mr. Ban da Mr. Kim sun kai ziyarar aiki tare a yankin Great Lakes a watan Mayu, abin da ya nuna muhimmancin inganta zaman lafiya da cigaba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China