in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana bukatar fuskantar da sauyin yanayi a kasar Sin
2013-11-19 14:44:18 cri
Jiya Litinin 18 ga wata, yayin da yake halarci babban taron sauyin yanayi da aka yi a birnin Warsaw na kasar Poland, shugaban tawagar wakilan kasar Sin Xie Zhenhua ya bayyana cewa, dukkan manufofin da kasar Sin ta gabatar kan batun sauyin yanayi sabo da bukatun kasar, sun dace da bukatar neman dauwamammen ci gaba a kasar.

Kuma wakilai na kasa da kasa, da na kungiyoyi daban daban da wasu wakilan kungiyoyi masu zaman kansu sun halarci taron tattaunawa kan sauyin yanayi da kasar Sin ta jagoranta. Yayin taron, Mr. Xie ya jaddada cewa, manufar da Sin ta gabatar game da sauyin yanayi ta dace da tsarin kwaskwarima na kasar Sin wajen bunkasa tattalin arziki.

Ya kuma kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bunkasa daga dukkan fannoni tare da rage fitar da gawayi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China