An kaddamar da cikakken zama na 37 na kwamitin gwamnatoci mai kula da sauye-sauyen yanayi na MDD
An kaddamar da cikakken zama na 37 na kwamitin gwamnatoci mai kula da sauye-sauyen yanayi na MDD wato IPCC a birnin Batumi dake kasar Georgia a jiya ranar 14 ga wata. An shafe kwanaki 5 wajen gudanar da taron, kuma wakilai fiye da 250 daga hukumomin gwamnatoci da bangaren fasaha na kasashe 110 suka halarta. A lokacin taron, wakilan za su kara tattaunawa kan sabbin abubuwan dake cikin rahoton bincike na 5 game da sauye-sauyen yanayi da kwamitin IPCC ya gabatar a birnin Stockholm na kasar Sweden a watan da ya gabata.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, za a kammala tattaunawa, kuma za a gabatar da dukkan abubuwan dake cikin rahoton bisa makatai daban daban kafin watan Oktoba na shekarar 2014. (Zainab)