Mista Wen ya nuna cewa, tun lokacin da aka shiga sabon karni na 21, har zuwa yanzu, ana ci gaba da samun bunkasuwar kimiyya da fasaha, bisa fannoni daban daban, hade da fannonin sadarwa, makamashi, kayayyakin zamani, ilimin halittu, kiyaye muhalli da dai sauransu. Shi ya sa ya kamata a ci gaba da inganta ayyukan gyare-gyaren tsarin kimiyya da fasaha, don su dace da hanyoyin bunkasuwar tattalin arzikin kasar, tare kuma da samun ci gaba da sauri, kan fannonin bunkasa muhimman ayyuka, manyan fasahohi da kuma sabbin kayayyaki.
Mista Wen ya kara da cewa, aikin ba da ilmi na da muhimmiyar ma'ana ga makowar kasar, shi ma tushe ne na bunkasar tattalin arziki, da zamantakewar al'umma. Kimiyya da fasaha na da mihimmanci ga bunkasuwar tattalin arziki, shi ya sa dole ne a mai da hankali kan aikin ba da ilmi, da kimiya da fasaha kan wannan hanya ta neman karin ci gaban kasa. (Maryam)