Majalisar gudanarwar ta kasar Sin ta amince tare da ba da sanarwa kan shawarar da wasu hukumomin kasar suka bayar kan kara yin kwaskwarima kan tsarin rarraba kaso ciki hadda kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima, ma'aikatar kudi, sashin kwadago da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a ta kasar Sin.
Sanarwar ta ce, tun lokacin da kasar Sin ta aiwatar da tsarin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje, ana ci gaba da kyautata tsarin rarraba kaso a matakai-matakai bisa halin da Sin ke ciki. A sa'i daya kuma, akwai sauran rina-a-kaba dangane da matsalar da ake fuskanta a wannan fanni, wato akwai gibi matuka tsakanin mazauna birane da mazauna kyauyuka, da kuma samun kudin shiga ba bisa doka ba, har ma wasu mutane na fuskantar mawuyacin hali. Sabili da haka, ya kamata, a ci gaba da yin kwaskwarima a wannan fanni, tabbatar da daidaici, adalci da zaman al'umma mai jituwa da karko da kuma ba da tabbaci ga moriyar jama'a. (Amina)