in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi a yi amfani da nasarorin da Sin ta samu wajen yin kwaskwarima don amfanawa jama'ar kasar
2012-07-24 11:11:41 cri

Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya jaddada a ranar 23 ga wata a nan birnin Beijing cewa, tilas ne gwamnatoci na mataki daban daban na kasar Sin su warware matsalolin da suka fi jawo hankalin jama'a, da ci gaba da samun nasara a fannonin bada ilmi, samun kudin shiga ta hanyar yin aiki, samun jinya a asibitoci, samun kulawa a yayin da aka tsuffa, samun wurin zauna, kana a yi amfani da nasarorin da aka samu sakamakon yin kwaskwarima da neman bunkasuwa wajen amfanawa jama'ar kasar, da kuma tabbatar da zaman rayuwar jama'a yadda ya kamata.

A gun bikin kaddamar da dandalin tattaunawa a tsakanin manyan jami'ai na ma'aikatu da lardunan kasar Sin da aka gudanar a wannan rana, Hu Jintao ya nuna cewa, an dogara kan manufar yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje wajen samun ci gaba cikin sauri a kasar Sin, tilas ne a ci gaba da aiwatar da wannan manufa wajen sa kaimi ga samun bunkasuwa a kasar. Game da yin kwaskwarima kan tsarin siyasa kuwa, Hu Jintao ya jaddada cewa, tilas ne a bi jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, jama'a su tsaida kuduri kan harkokinsu, sarrafa harkokin kasar bisa doka, samun bunkasuwa a dukkan fannoni, tabbatar da tsarin demokuradiyya ga jama'ar kasar, yin zabe bisa doka, tsara manufofi da gudanar da ayyuka da sa ido bisa demokuradiyya, dora muhimmanci kan muhimmiyar rawa da dokokin kasar suke takawa kan harkokin kasar da zamantakewar al'ummar kasar, tabbatar da ikon dokokin kasar da adalci da kuma hakki da 'yancin kai na jama'ar kasar bisa doka.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China