A wajen ganawar, Mista Li ya ce, nahiyar Afirka tana kunshe da fatan alheri, kana za a iya hangen wani yanayi mai kyau wajen yin hadin kai a tsakanin bangarorin Sin da Afirka. Don haka, kasar Sin, a cewarsa, za ta tsaya kan manufofin kiyaye zaman lafiya, neman ci gaba, kokarin hadin kai, da tabbatar da moriyar juna, a kokarinta na neman amfanawa juna bisa yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, ta yadda za a kara kyautata huldar dake tsakanin bangarorin 2.
Har ila yau Mista Li yayi bayanin cewa, JKS na son kara yin mu'amala da hadin gwiwa tare da majalisar jam'iyyun Afirka, da kuma jam'iyyun siyasa na kasashen Afirka, don more damar samun ci gaba, gami da musayar ra'ayi kan fasahohin raya kasa.
A nasa bangare, shugaban majalisar jam'iyyun Afirka, kuma babban magatakardan jam'iyyar PF ta kasar Zambia, Mista Wynter Kabimba, ya ce kasar Sin ita ce abokiyar Afirka ta zahiri, ganin yadda take kokarin rufa ma kasashen Afirka baya kan yunkurinsu na neman ci gaba da samun zaman lafiya. Saboda haka a cewar shi, majalisar jam'iyyun kasashen Afirka zata dukufa kan kokarin kyautata huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.(Bello Wang)