A yayin ganawar, mista Xi ya jaddada cewa, yanzu dangantaka tsakanin mashigin tekun Taiwan tana kan wani sabon matsayi, tare da fuskantar muhimmin zarafi. Dole ne a rika bunkasa dangantaka tsakanin mashigin tekun Taiwan, da zurfafa babban tushen bunkasa dangantaka tsakaninsu a fannonin siyasa, tattalin arziki, al'adu, da zamantakewar al'umma, a kokarin sa kaimi ga raya dangantakar zuwa wani sabon mataki.
A nasa bangaren, Wu ya jaddada cewa, tsayawa tsayin daka kan manufar "kasar Sin daya tak a duniya", da yaki da kawo wa kasar Sin baraka, matsayi guda ne da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyar KMT suke kasance a kai, kuma babban tushe ne na bunkasa dangantaka tsakanin mashigin tekun Taiwan cikin lumana. Ya kara da cewa, kamata ya yi bangarorin biyu su karfafa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki, da mu'amala a fannonin zamantakewar al'umma da al'adu, ta yadda jama'a za su kara cin gajiya yadda ya kamata.(Fatima)