Sharhin ya zayyana yadda aka amince da kudurin wajen bunkasa tsarin gyare-gyaren al'adu na Sin da ci gaban al'adu irin na gurguzu a zaman babban kwamitin tsakiya na JKS na 17 wanda aka kammala a ranar Talata.
Kudurin ya kasance wani jagora ga tsarin gyare-gyaren ci gaban al'adu da Sin za ta aiwatar a nan gaba, sharhin ya nuna cewa, hakan ya nuna yadda kwamitin tsakiya na JKS ya mai da hankali kan manufarta da halin da ake ciki a cikin gida da kasashen waje kana da fahimtar jam'iyyar wajen gina tsarin al'adu mai tasiri.
Sharhin ya jaddada cewa, wajibi ne Sin ta bi tafarkin raya al'adu irin na gaurguzu sau da kafa yayin da take kokarin bunkasa tsarinta na al'adu saboda matsayi da tasirin da al'adun ke da shi wajen jan ragamar kasa da kuma tasirin al'adun kasar Sin a duniya. (Ibrahim)