in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala zagayen farko na neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Turai, da nahiyar kudancin Amurka, da nahiyar tsakiya da arewacin Amurka da kuma yankin Caribbean
2013-10-25 15:56:11 cri

Nahiyar tsakiya da arewacin Amurka da yankin Caribbean:

Bisa jadawalin gasar fidda zakarun wannannahiya, kungiyoyi uku da suke kan gaba a nahiyar tsakiya, da arewacin Amurka da yankin Caribbean, za su shiga gasar cin kofin duniya kai tsaye, yayin da kuma kungiyar da ta zama a matsayi na hudu za ta shiga zagaye na biyu.

Kafin wasan karshe, Amurka da Costa Rica sun samu tikitinsu kai tsaye, yayin da Mexico da Honduras ke neman zama matsayin uku a yankin. A wasan karshe, Costa Rica ta lashe Mexico da ci biyu da daya, ita kuma Honduras ta yi kunnen doki da Jamaica da ci biyu da biyu. Don haka, Honduras ta zama a matsayi na uku, tare da samun damar shiga gasar cin kofin duniya a wannan karo kai tsaye. Inda ita kuma Mexico ta zama a matsayi na hudu, za kuma ta shiga zagaye na biyu.

Bisa tsarin gasar kungiyar da ta zama a matsayi na hudu a nahiyar tsakiya da arewacin Amurka da yankin Caribbean, za ta yi wasa da kungiyar da ke matsayi na farko a yankin Oceania don neman shiga gasar cin kofin duniya a wannan karo. Wato hakan na nuna cewa kasar Mexico za ta yi wasan da New Zealand, a kokarin kasashen Biyu na samun gurbin shiga kasar cin kofin duniyar dake tafe.

Ya zuwa yanzu dai, an fitar da kungiyoyi 21 da suka samu damar shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Brazil a shekarar 2014 mai zuwa. Za kuma a fitar da jimillar kungiyoyi 32, da za su shiga gasar a watan Nuwanba mai zuwa. Inda kuma a watan Disamba mai zuwa, ake fatan raba rukunonin gasar. (Zainab)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China