in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala zagayen farko na neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Turai, da nahiyar kudancin Amurka, da nahiyar tsakiya da arewacin Amurka da kuma yankin Caribbean
2013-10-25 15:56:11 cri

Nahiyar kudancin Amurka:

Yanzu kuma bari mu waiwayi kulaflikan dake nahiyar kudancin Amurka, inda a ranar 16 ga wata, suma suka kammala wasannin zagayen farko na nahiyar, na share fagen shiga gasar cin kofin duniyar dake tafe. Bisa jadawalin wasannin da aka buga, kungiyoyi 4 na sahun gaba a wannan nahiya, sun kuma samu damar shiga gasar cin kofin na duniya kai tsaye, sa'an nan kungiyar da ta zama ta Biyar za ta fito ne bayan wasannin zagaye na biyu.

Kafin wasan karshe, Argentina da Columbia sun samu shiga jerin masu buga gasar cin kofin duniya kai tsaye. Bayan da a wasan karshe, Uruguay ta lashe Argentina da ci uku da biyu, sai Chile ta lashe Ecuador da ci biyu da daya, sannan kuma Columbia ta doke Paraguay da ci biyu da daya. Don haka, Chile ta zama a matsayin uku, inda ta samu damar shiga gasar cin kofin duniya kai tsaye. Uruguay da Eduador sun samu maki iri daya, amma Eduador ta fi Uruguay cin kwallaye a zagayen farko, don haka Eduador ta zama a matsayi na hudu, za kuma ta buga gasar cin kofin duniya kai tsaye, yayin da ita kuma Uruguay za ta shiga zagaye na biyu na gasar, domin neman cimma nasarar samun gurbin da take nema, tsakanin ta da kungiyoyi biyu na nahiyar Asiya, wadanda suma ke a matsayi na uku a rukunin su. Wadannan kungiyoyi biyu na nahiyar Asiya su ne Uzbekistan da Jordan. Dama dai tun cikin watan Satumbar da ya gabata bayan da aka buga wasanni biyu a tsakaninsu, Jordan ta lashe Uzbekistan. Don haka Uruguay za ta yi wasa da Jordan a yunkurin ta na neman shiga gasar cin kofin duniyar dake tafe.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China