A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar bayan ganarwasu a birnin Pretoria, shugabannin na Sin Xi Jinping da na Afrika ta Kudu Jacob Zuma gaba dayansu sun amince da cewa, dangantakar hadin gwiwa tana daya daga cikin manyan jigon karfafa zumunci ga ko wace kasa, don haka kasashen biyu suka yi alkawarin inganta wannan fanni zuwa wani sabon matsayi.
A ta fuskar sauran kasashen duniya kuwa, Sin da Afrika ta Kudu sun sha alwashin martaba 'yanci da ra'ayin sauran kasashe masu tasowa sannan kuma za su saka tsari da ka'idoji da ba za su takura ma wadannan kasashen ba a cikin daidaito.
Sai dai kuma shugabannin sun yi kira ga sauran kasashen duniya da su mai da hankali sosai tare da samar da taimakon da ya kamata ma nahiyar Afrika, su mutunta kokarin kasashen Afrika wajen warware matsalolin da suka shafi nahiyar tasu da kansu sannan kuma su taimaka masu wajen inganta kokarin da suke yi ta hanyar samar da ci gaba da kansu.(Fatimah)