Xi Jinping kuma ya kara da cewa, yau nahiyar Afrika ta zama daya daga cikin wasu yankuna da suke fi samu bunkasuwar tattalin arziki a duniya, kasar Sin kuwa tana ci gaba da samu bunkasuwa yadda ya kamata, dalilin da ya sa bangarorin biyu suke fuskantar sabon zarafi mai kyau wajen raya dangantakar dake tsakaninsu. Mr Xi ya bayyana yadda Sinawa za su raya dangantakar dake tsakaninsu da jama'ar Afrika bisa wata kalma ta sahihanci. Kuma yana jaddada cewa, Sin sahihiyar kawa ce ga nahiyar Afrika har abada, kuma ba za ta canja wannan matsayin da take dauka ba duk da cewa za ta ci gaba da samun karin bunkasuwa da daga matsayinta cikin duniya. Sin na nacewa ga samu bunkasuwa tare da kasashen Afrika, Sin za ta cika alkawarin da ta yi wa kasashen Afrika. Kuma game da sabbin matsaloli da za su bullo cikin hadin gwiwa da za su yi, Sin za ta warware su yadda ya kamata bisa ka'idar mutunta juna da kawo moriyar juna. (Amina)