in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Zimbabwe Robert Gabriel Mugabe
2011-11-16 20:14:08 cri

A ran 16 ga wata, a birnin Beijing, mataimakin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Zimbabwe Robert Gabriel Mugabe.

Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna godiya ga kasar Zimbabwe da ta nace ga bin manufar Sin daya tak a duniya, Sin ta nuna goyon baya ga kokarin da kasar Zimbabwe take yi wajen neman hanyar samun bunkasuwa wadda ke dacewa da halin da kasar take ciki. Dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu wani muhimmin abu ne, ya kamata kasashen biyu su kiyaye dangantakar da ke tsakaninsu. Kuma kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Zimbabwe wajen kara yin mu'amala da kara yin hadin gwiwa, da kara bunkasa dangantaka a tsakaninsu.

Robert Gabriel Mugabe ya bayyana cewa, kasar Sin aminiya ce ga kasar Zimbabwe, don haka, kasar Zimbabwe tana mai da hankali sosai kan aikin bunkasa dangantaka a tsakanin kasashen biyu, haka kuma tana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannoni aikin gona, hako ma'adinai, da kuma kyautata manyan ayyukan yau da kullum, don kara kyautata huldar da ke tsakanin kasashen biyu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China