in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bundesliga mai tsari na 'Kwaminisanci'
2013-10-01 21:06:13 cri

Sakamakon wannan tsari mai kyau da ake bi, da ci gaban tattalin arzikin kasar Jamus, kuloflika 18 na Bundesliga, tun a kakar wasan da ta wuce, sun yi ta kokarin zuba jari tare da samun riba, jarin da yawansa ya kai Pound miliyan 154, wanda ya zarce Pound miliyan 98 da Premier League na kasar Birtaniya ya samu. Da hakan Bundesliga ya zama tsarin gasannin wasan kwallon kafa mafi samun riba a kasashen Turai. Yayin da kuma kulob din Bayern Munich ya yi shekaru 20 yana ta samun riba ba tare da hasara ba, matakin da ya sanya ake wa kulob din lakabi da kulaf mai 'lafiyar jiki' a fadin nahiyar Turai.

Hakika dai, yanzu kafofin watsa labaru na kasashe daban daban suna kokarin binciken tsarin Bundesliga. A yayin da hukumar wasan kwallon kafa ta nahiyar Turai ke kokarin tabbatar da daidaito a fannin samun kudi tsakanin kuloflika daban daban, tsarin Bundesliga ya riga ya zama wani abin koyi.

Sepp Blatter, shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta Turai, ya taba bayyana Bundesliga a matsayin tsarin wasanni mafi samun nasara a duniya. Idan an dubi tsarin wasanni na wasu kasashen Turai, za a ga Premier League na kasar Birtaniya ya zama wani filin wasan damben jari hujja, inda masu kudi suke wasa da kuloflikan da suka mallaka. Sa'an nan gasar La Liga ta kasar Spain ta zama dandalin kuloflika 2, wato Real Madrid da Barcelona. Yayin da Real Madrid take kashe makudan kudi wajen sayen fitattun 'yan wasa kamarsu Cristiano Ronaldo, da Gareth Bale, yayin da a hannu guda wasu kananan kuloblikan kasar da dama suke kasa biya ma 'yan wasansu albashi.

A iya cewa, a lokacin da tsarin wasannin sauran kasashen Turai ke samun nakasu, tsarin Bundesliga a daya bangaren na dada samun ci gaba.(Bello Wang)


1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China