130905-Me-ya-hana-Wayne-Rooney-zama-dan-wasa-mafi-kwarewa-Bello.m4a
|
A yau za mu mai da hankali ne ga sharhi kan wani shahararren dan wasan kwallon kafar kasar Birtaniya, wanda ke taka leda a kulob din Manchester United, wato Wayne Rooney.
Wayne Rooney wanda ke cikin 'yan wasan da suka taka leda a gasar cin kofin zakarun Turai ta bara, an ce a waccan lokaci, akwai dan sabani tsakanin shi da mai horar da 'yan wasan kungiyar Manchester United Sir Alex Ferguson. Ban da haka, akwai jitar-jitar cewa Rooney zai canza shekarsa zuwa wani kulob na daban.
A wannan kakar wasa da muke ciki, Rooney ya fara da kasancewa a tebirin canji. Kana duk da cewa yana taimakawa 'yan kungiyarsa cin kwallaye, bai taba taya su murnar samun nasarar jefa kwallayen ba. Irin wannan hali da Rooney ke nunawa ya sa aka fara gano alamun yiwuwar barinsa kulaf din Manchester a nan gaba.
Hakika dai, idan an waiwayi yadda Rooney ya taka leda a kulob din Manchester United a shekarun baya, za a iya yarda da cewa sannu a hankali ya fara samun koma baya sosai.
A kakar wasa ta shekarar 2004 zuwa ta 2006, Wayne Rooney ya kasance a matsayin dan wasan da ke hada 'yan wasan gaba da 'yan wasan tsakiya. A lokacin 'yan wasan da ke dab da Rooney, dukkansu 'yan gaba, da kuma tsakiya ne, wadanda kuma ba su kware sosai wajen sarrafa kwallo ba. Don haka, Rooney wanda fasaharsa ta shafi bangarori daban daban, ya fara zama ginshikin kungiyar.
Sa'an nan a shekarar 2006, Rooney ya gamu da wata babbar matsala, inda raunin da ya ji a wannan lokaci, da yadda ya taka Ricardo Carvalho na kungiyar Real Madrid, suka sauya hanyarsa a fagen taka kwallo. A kuma wannan lokacin ne, Cristiano Ronaldo ya samu damar maye gurbin Rooney, a matsayin ginshikin dan wasan kulaf din na Manchester United wajen gwada basirar taka leda. Yayin da kuma Wayne Rooney, da Carlos Tévez suka zama masu tallafawa shi C. Ronaldo din a gaba.
A kakar shekarar 2009, C. Ronaldo ya bar kulob din Manchester United, don haka Rooney ya sake samun wani matsayi mai muhimmanci, tamkar sarki a kulob din nasa, inda ya yi kokari matuka wajen taka matsayin gaba ta tsakiya, tare da yin amfani da karfin jikinsa, wajen tinkarar 'yan wasan bayan kungiyoyin hamayya, kamar dai yadda hakan ya yi daidai da sananniyar fasahar kocin Ferguson, ta maida kora nan take ga abokan karawa.