in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bundesliga mai tsari na 'Kwaminisanci'
2013-10-01 21:06:13 cri

Irin ka'idar da aka bayyana ta filla-filla karkashin manufar dake da lakabin '50+1' da hukumar kwallon kafa ta kasar Jamus ta gabatar, wadda ta hana daidaikun mutane, ko wani rukunin mutane zuba jari da ya wuce kaso 51%, na hannayen jarin ko wane kulob. Karkashin wannan manufa, an tabbatar da cewa kuloflikan kasar Jamus, za su ci gaba da kasancewa na jama'a masu sha'awar kwallon kafa. Kana kulflikan a nasu bangaren ba za su kashe kadade fiye da kima ba, sakamakon yadda aka kayyade harkar zuba musu jari.

Ban da haka, hukumar Bundesliga ta kayyade cewa, daidaikun mutane, da kamfanoni, ba za su samu damar mallakar hannun jari mai rinjayen na ko wane kulob ba, sai dai bayan shafe shekaru 20 ana jan ragamar kulaf din.

Irin wannan ka'ida da ta shafi ikon mallakar kaso mai yawa na jarin kulaflika, ta kori masu sha'awar zuba jari da dama na kasashen waje, wadanda ke da makuden kudaden sanyawa a kulaflika. Wannan mataki ya sa babu wasu kuloflika masu kudi sosai a Bundesliga, wadanda zasu yi kafada-da-kafada da kulaflika irin su Manchester City dake kasar Birtaniya.

Ma iya cewa tsarin Bundesliga ya kasance tsarin da ya fi tabbatar da daidaito tsakanin kuloflika daban daban, idan aka yi la'akari da tsarin da ake bi wajen raba kudaden da ake samu, ta hanyar nuna gasannin wasan kwallon kafa ta kafafen telabijin.

Ga misali a kakar wasa da muke ciki, tsarin Bundesliga ya samu Euro miliyan 628, daga gidajen telabijin da suka nuna wasanninsa. kuma yayin da ake rarraba kudi tsakanin kuloblika daban daban, an yi kokarin kiyaye gibin dake tsakaninsu, duk da cewa dukkan kuloblikan suna samun karuwar kudade. Ga misali, Bayern Munich, wanda ya kasance daya daga kuloblika mafiya karfi a tsarin Bundesliga, ya samu Euro miliyan 33.2, yayin da SpVgg Greuther Furth, da ya kasance a karshen jadawalin kuloflikan Bundesligar ya samu Euro miliyan 16.6.

Idan an kwatanta kudin da kuloflikan 2 suka samu, za a ga na Bayern ya ninka na Furth sau 2, kana gibin dake tsakanin su na Euro miliyan 10 da wani abu ne kawai. Da an kwatanta kudinsu da na kuloflikan sauran kasashe, za a ga yawan kudin ya kasance a matsakaicin matsayi.

A gasar La Liga ta kasar Spain ga misali, kuloblika Real Madrid da Barcelona su ne suka yi awon gaba da rabin daukacin kudin da aka samu a gasar baki daya, wanda yawansa ya ninka na kulob din dake karshe a jadawalin gasar har sau 19. Kana a gasar Serie A ta kasar Italiya, Juventus da wasu sauran kuloflika masu karfi, sun kulla yarjejeniya da gidajen telabijin kai tsaye, ta yadda suka samu rinjayen kudin nuna wasanni.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China