in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bundesliga mai tsari na 'Kwaminisanci'
2013-10-01 21:06:13 cri


A yau za mu mai da hankali ne kan wata gasa mai muhimmanci a fannin wasan kwallon kafa, wadda ake wa lakabi da Bundesliga, wato gasar da ta shafi kuloflikan kwallon kafa na kasar Jamus.

Idan muka koma ga tarihi, za mu ga a shekarar 1818 aka haifi wani masanin harkokin gudanar da mulki mai suna Karl Marx a kasar Jamus, wanda daga bisani ya kirkiro tsarin siyasa na Kwaminisanci, tsarin da ya fi mai da hankali kan samar da daidaito ga al'umma, da samun ci gaban al'umma bai daya. Tsarin da watakila ya yi tasiri kan hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Jamus. Domin a yanzu haka ana iya ganin wani tsarin da ya yi kama da Kwaminisanci da ake bi a gasar kulaflikan kasar ta Bundesliga.

Mun san cewa a kasashe daban daban an fi samun kuloflika masu zaman kansu, wadanda suke kasancewa karkashin mallakar wasu mutane masu kudi. Har ma akwai wasu daga cikinsu dake karkashin mallakar 'yan kasuwa na kasashen waje. Ga misali kuloflikan Manchester United, da Liverpool na kasar Birtaniya na ciki jerin irin wadannan kulaflika. Amma a kasar Jamus, akwai ka'idoji na musamman ga 'yan kasuwa, wadanda ke son zuba jari cikin kuloflikan Bundesliga.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China