in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasanni masu ban sha'awa
2013-07-25 17:34:37 cri

Wasanni ba dukkansu an yi su ne domin takara da wani, da fid da gwani ba. Wasunsu a kan yi su ne domin faranta rai, da kulla abokantaka, gami da motsa jiki. A yau ma za mu gabatar da wasu wasanni masu ban sha'awa da za a iya gwada su a zamanmu na yau da kullum.

1)tseren gudu tare da daukar kwallon tebur

Wani irin gudun ba da sanda ne, sai dai ba sanda ko kulki ake musaya a tsakanin 'yan wasan ba, a maimakon hakan a kan mika kwallon tebur ne. A kan yi wasan kamar haka: dan wasa yana rike abin buga kwallon tebur ne a hannun sa, sa'an nan ya sanya kwallon a tsakiyar wannan dan faifai, ya kuma yi kokarin hana ta fadowa ta hanyar daidaita zamanta sannu a hankali. Sai kuma ya shiga gudu har tsawon mita 10 da wannan kwallo dake kan abun bugun kwallon tebur, har ya kai wani kwando da aka tanada, domin jefa kwallon ta tebur ciki. Sa'an nan wani dan wasan daban zai dauki wannan kwallo, don ya ci gaba da gudu da ita kamar yadda wanda ya gabace shi ya yi. Idan kwallo ya fadi kasa yayin da ake gudu, dan wasan zai koma inda ya fara gudu, domin ya sake.

Za a iya gudanar da gasar a tsakanin kungiyoyi 2, wadanda ko waccensu ka iya kunsar mutane 8. Daga karshe kungiya da ta fi saurin gama gudun ba tare da matsala ba, ita ce za ta zamo wadda ta yi nasara a gasar.

2)Gudun ba da sanda na mita 100 na tsallake shingaye

Wannan ma gudun ba da sanda ne, sai dai ana yinsa ne, tare da tsallake wasu shingaye, wadanda ake yin su ta hanyar amfani da karamar kujera, da igiya, da balo. Daga inda za a fara gudu, zuwa wani wuri mai tazarar mita 50 za a ajiye balo din, sa'an nan tsakanin balon da layin fara gudu za a sanya karamar kujera wadda ake bukatar dan wasa ya tsallake, sa'an nan ya bi ta karkashin igiya, wadda za a rike gefunanta guda biyu, domin 'yan wasa su bi ta karkashinta.

Ana yin wasan kamar haka: 'yan wasa suna rike sanda a hannu, su yi gudu, sa'an nan za su tsallake karamar kujera, da bita karkashin igiya. Daga bisani su zagaye balon, su sake bi ta karkashin igiyar, su tsallakewa kujera, domin su ba da sanda ga abokin wasansu. Za kuma a maimaita hakan tsakanin 'yan wasa 12, cikin kungiyoyi 2. Kungiya da ta fi saurin gama gudun, ita ta yi nasara ke nan.

3) Takarar samun sukarin Lollipop

'Yan wasa 2 suna tsayawa kusa da juna, daya ya fuskanci bangaren gabas, yayin da dayan ya fuskanci yamma, inda za su hada hannuwan su ta baya, ta yadda daya zai iya goyan dayan. Sa'an nan a gaban ko wanensu za a sanya wata yarinya wadda take rike da sukarin Lollipop a hannu. Daga bisani, bisa umarnin alkalin wasa, 'yan wasan 2 za su fara kokarin yin gaba, tare da janye abokan karawa ta baya, don ya karbi sukarin da yarinyar ke rike da shi da bakinsa. Wanda ya fara samun karbar sukarin shi ne ya yi nasara ke nan.

4) Wasan kwallon badminton a kungiyance

A kan shirya wannan wasa ne ta hanyar bukatar mutane 8, wadanda za a kasa su cikin kungiyoyi 2. Sa'an nan 'yan wasa 4 dake cikin ko wacen kungiya, za su buga kwallon badminton na karba-karba, wato daya ya buga kwallo, sa'an nan ya tsaya a gefe, domin dayan ma ya shiga tsakiyar fili, domin buga kwallon da aka bugo musu. Ban da batun nan na sanya 'yan wasa takwas su buga kwallo tare, wasan ya yi kama da wasan kwallon badminton da ake gudanar da shi a yau da kullum.

5) Gudun hada kafa

Shi kuwa wannan wasa ana gudanar da shi ne tsakanin kungiyoyi, wadanda ko wacensu ta kunshi mutane 5. Za a sanya mutanen 5 su tsaya kan layi daya, daga bisani za a daure kafafuwansu da igiya don hada biyu-biyunsu tare. Bayan da alkalin wasa ya ba da alama, dukkan kungiyoyin da suka halarci wasan za su fara gudu, kana wadda 'yan wasanta suka fi saurin kaiwa layin karshe itace ta yi nasara.

6)karamin Bawling

Za a ajiye wasu ababen sha kamarsu Coke, Sprite, ko kuma nono, bisa tsarin da ake bi wajen ajiye kwalaben Bawling. Sa'an nan masu shiga wasan za su gara wata kwallon tennis daga nesa. Idan kwallon da aka gara ta kayar da kwalaba ko kwalaben da aka jera suka fadi kasa, to, za a baiwa dan wasan abin shan da ya fadi a matsayin kyauta. Amma idan kwallon da aka jefa bai samu kome ba, wanda ya yi jifan zai yi gudu, har da zagaya fili.

7) wasan ja-in-ja da igiya

Ana sanya kunkiyoyi 2 su shiga gasar, wadanda ko wacensu na da 'yan wasa 15. Sa'an nan ko wace kungiya za ta kama gefe daya na igiyar, su yi kokarin ja da karfin gaske, don neman janyo abokan karawar su zuwa bangaren da suke.

8) wasan gudun ba da sanda da baya da baya

Wannan ma gudun ba da sanda ne, sai dai maimakon shekawa a guje ta gaba, 'yan wasan suna tseren ne da baya da baya, kafin kaiwa ga wanda za a baiwa sanda ya ci gaba daga inda aka tsaya. Alkalin wasa zai hana a juya jiki yayin da ake gudu.

9) wasan gudun kora kwallaye

Za a sanya dan wasa ya yi amfani da sanda, don tura kwallaye 2 gaba. Kwallayen 2 sun hada da ta Basketball guda, da kuma ta Volleyball daya. Dan wasa zai yi kokarin bin wata hanya domin tura su, har ya kai su bayan layin karshe, kamar yadda makiyaya su kan kora raguna don su shiga gidansu. Shi ya sa ma ake wa wannan wasa lakabi da "wasan kora raguna".

Yayin da ake kora kwallayen biyu, idan wani daga kwallayen ya karkata, ya fito daga hanyar da ake bi, to kokarin da dan wasan yake yi, ya ci tura ke nan, za a hana shi ci gaba da wasan. A kan iya sanya mutane 2 ko 3 su shiga wasan a lokaci guda, kana wanda ya fi saurin kai raguna gida ya ci nasara a gasar ke nan.

10) wasan buga Jian-zi

Jian-zi wani irin abun wasa ne na musamman, wanda ake yawan amfani da shi a nan kasar Sin. Siffarsa ta yi kama da kwallon badminton mai dauke da gashin tsuntsu, wato ba wadda ke da siffar Kwando ba.

Jian-zi yana da dan kullutu mai nauyi a kasa, da gashin tsuntsu a sama. A kan buga Jian-zi da kafa don ya tsalle sama, sa'an nan a sake tarar sa da wani bugun da kafa wato lokacin daya sauko ke nan. A yi ta yin hakan ana kirgawa,dan wasa zai yi iya kokarin sa ya hana wannan abun wasa faduwa kasa.

A wannan wasa da muke batu a kan sa, za a yi zanen wata da'ira a kasa, san nan a yi kokarin buga Jian-zi, don ya sauka kan daya daga da'irorin da aka zana. Idan dan wasa ya buga Jianzi har ya sauka cikin karamar dari'ar dake tsakiyar zanen, to sai a bashi maki da ya fi yawa. Idan kuwa Jian-zi ta shiga da'irar dake waje, za a samu maki da bai kai wancan yawa ba. Ta haka za a iya kirgar makin da 'yan wasan suka samu a ko wanne karon da ake buga Jian zi, a kwatanta su don fidda gwani.

11) Gasar tsere da kwallo a baya

Za a sanya mutane biyu-biyu su tsaya daya ya fuskanci gabas, dayan ya fuskanci yamma, sai a sanya kwallon kwando a tsakanin bayan su, 'yan wasan za su matse wannan kwallo su hana ta faduwa, su kuma yi gudu da ita, ba tare da ta fadi ba. Za a iya shirya wannan tsere da sauran kungiyoyi domin fidda gwani. Wandanda suka cimma kaiwa ga layin karshe kafin saura su ne wadanda suka ci nasara a wasan.

12) tseren masu dauke da hula hoop

Kawanyar gare-gare (wato hula hoop a Turance) wani irin abin wasa ne, wanda ake yawan yin amfani da shi a wurare daban daban na duniya don motsa jiki. Yayin da ake wasan kawanyar hula, a kan sanya gare-garen a kugu, a yi ta juya shi ta hanyar kewaya kugu, ko karan jikin mai wasan, sa'an nan dan wasa zai hada wannan dabara ta juya gare-garen a jikin sa da kuma gudu a lokaci guda, zai yi wannan gudu izuwa inda 'yan kugiyar sa suke, idan gare-garen dake jiki ya fadi, sai a tsaya a nan a maida shi jiki, a kuma ci gaba da juya shi, da gudu a tare.

A yayin wannan wasa da muke batu a kan sa a yau, za a sanya 'yan wasa su yi tsere tare da kada jikin su, ta yadda gare-garen da suke dauke dashi zai rika juyawa, ba tare da ya fadi ba, yayin da suke gudu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China