Hakika, kulob din Bayern ya taba yin kira ga hukumar Bundesliga don ta yi koyi da tsarin La Liga da na Serie A, don kara gibin dake tsakanin kuloflikan ta fuskar rabon kudade, amma hukumar ta ki yarda da hakan, bisa la'akari da moriyar sauran kuloflikan kasar. Ta wannan za mu iya ganin yadda hukumar take kokarin kiyaye daidaito tsakanin kuloflika daban daban.
Idan a kan kalli gasannin Bundesliga, tilas za a lura da wani yanayi mai burgewa, wato a ko wace gasa ana iya samun jama'a 'yan kallo da yawa, wadanda suke cika kujerun dake dab da filin wasa. Hakan kuwa baya rasa nasaba da arhar tikitin kallon gasar Bundesliga, wanda ke baiwa karin jama'a damar kallon wasa a dab da fili. Amma idan muka kalli tsadar tikitin kallon wasannin Premier League na kasar Birtaniya, zamu ga ya dara na Bundesliga matuka.
An ma ce, a kakar wasannin da ta wuce, farashin tikitin kallon karawa tsakanin Arsenal da Bayern a gasar zakarun Turai da aka gudanar a kasar Birtaniya, ya yi daidai da na tikitin kallon dukkan gasannin da kulaf din Bayern ya shiga a kasar Jamus na shekara guda.
Ban da kyautatawa jama'a masu sha'awar wasan kwallon kafa, kuloflikan Bundesliga, musamman ma kuloflika masu karfi irinsu Bayern, su kan yi kokarin taimakawa sauran kuloflika. Alal misali, Bayern Munich, wanda ake kallonsa a matsayin kulob din da ya fi son tallafawa saura, ya kan yi gasar sada zumunta da wasu kungiyoyin dake bakin rushewa, inda yake basu dukkan kudin da aka samu yayin wasan, domin su fita daga mawuyacin halin da suke ciki. Ta wannan hanya, Bayern ya taimaki kulaflikan Alemannia Aachen, St Pauli, Rostock Hansa, da dai sauran su.
Idan muka sake waiwayar tarihi za mu ga cewa, a kasar Jamus ne, aka haifi wasu mashahuran masana irinsu Immanuel Kant, da George Hegel, da Karl Marx, wadanda suka kware wajen tunani, da kirkiro tsari mai inganci na samar da daidaito tsakanin al'umma. Saboda wannan fasahar da al'ummar Jamus suka gada ne, ya sa kasar ta samu ci gaba sosai a fannin kirkiro tsarin wasan kwallon kafa. Ciki hadda manufar '50+1', da dabarar raba kudin nuna gasanni ta telabijin, matakin da ya shaida ra'ayin jama'ar kasar na mai da hankali kan daidaita al'umma da tabbatar da adalci.