in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna murna da nasarar da jam'iyyar CDU/CSU ta cimma a zaben majalisar dokokin kasar Jamus
2013-09-23 20:33:44 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Litinin 23 ga wata cewa, kasar Sin ta yi murna da nasarar da jam'iyyar CDU/CSU dake karkashin jagorancin shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel ta cimma a zaben majalisar dokokin kasar Jamus.

Ban da wannan kuma, Hong Lei ya ce, kasashen Sin da Jamus abokai ne bisa manyan tsare-tsare, kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu ya dace da moriyar kasashen biyu. Kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwa tare da sabuwar gwamnatin kasar Jamus wajen inganta dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China