in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Jamus sun ba da wata hadaddiyar sanarwa kan ziyarar Li Keqiang a kasar Jamus
2013-05-27 16:49:20 cri

Sin da Jamus sun ba da wata hadaddiyar sanarwa kan ziyarar Li Keqiang a kasar Jamus a ran 26 ga wata, inda aka nuna cewa, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya kai ziyarar aiki a kasar Jamus daga ran 25 zuwa 27 ga wata bisa gayyatar da aka yi masa. Wannan karo ne na farko da Li Keqiang ya kai ziyara zuwa kasashen waje tun bayan hawan sa kujerar firaministan kasar Sin. Shugabannin kasashen biyu sun yi musayar ra'ayi sosai kan dangantakar da ke tsakanin bangarori 2 da wasu batutuwan kasa da kasa da suke jawo hankalinsu duka, tare kuma da cimma matsaya daya kan muhimman batutuwa da dama.

Sanarwar ta ce, bangarorin biyu sun nanata wajibcin mutunta juna kan ikon mallakar kasa da cikakken yankin kasa, da kuma dukufa kan warware rikicin dake faruwa a shiyya-shiyya ko duniya cikin lumana. Bangarorin biyu kuma na fatan kara fahimtar juna kan hanyar da suke bi na samun bunkasuwa, har ma da kara amincewa da juna a fannin siyasa ta yadda za su ingiza dangantakar dake tsakaninsu cikin dogon lokaci.

Dadin dadawa, a cikin sanarwar, an ce, bangarorin biyu sun yanke shawarar tabbatar da dangantakar abokantaka tsakanin birane da garuruwan kasashen biyu, da kuma kara hadin gwiwa tsakaninsu a fannoni sha'anin gona, gandun daji, abinci, kiyaye hakkin masu sayayya, ba da tabbaci ga samun isasshen hatsi da kiyaye muhalli da sauransu.

Ban da haka, sanawar ta ce, kasashen biyu na cimma matsaya kan yaki da manufar ba da kariya, kuma suna fatan warware wasu bambanci ra'ayi kan batutuwan da suka shafi aikin sadarwa ta hanyar yin shawarwari.

Ban da haka, firaministocin biyu sun kaddamar da wani biki mai taken "Harsunan Sin da Jamus" na tsawon shekara daya. A ganinsu, Sin da Turai sun kasance muhimman kasashe ne a duniya, kuma sun kasance manyan abokai dake taka rawa wajen ciyar da zaman lafiya, wadata da karko gaba a duniya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China