in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kolin shugabannin kamfanonin musulmi na kasa da kasa a birnin Yinchuan na Sin
2013-09-14 17:37:40 cri

An bude taron kolin shugabannin kamfanonin musulmi na kasa da kasa na shekarar 2013 a birnin Yinchuan na kasar Sin, taron da hukumar birnin Yinchuan ta dauki nauyin shiryawa.

A matsayin wani muhimmin shiri cikin taron baje kolin kasar Sin da kasashen Larabawa na shekarar 2013, shugabannin musulmi da suka halarci taron daga kungiyoyin musulmi, wakilan gwamnatocin kasashen Larabawa, Amurka, Faransa, Rasha da dai sauran kasashe guda 37 ne suka halarci wannan taro. Bugu da kari, mahalarta taron sun yi tattaunawa kan batutuwan da suka shafi sada zamunci, cudanya, hadin gwiwa da kuma cimma moriyar juna a fannonin cinikayya, da zuba jari tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa da kuma yankunan musulmi. Har ila yau an tattauna batutuwan da suka jibanci hadin gwiwar da ke tsakanin kamfanonin musulmi na kasa da kasa, da kebabben yankin masana'antun da gwamnati ta daukawa masa haraji birnin na Yinchuan, da kuma ci gaban tattalin arzuki da harkokin yawon shakatawa tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa da dai sauran fannoni daban daban. (maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China