Dalibai daga makarantun addinin musulunci da ke birnin Niamey za su nuna wasu al'adun musulunci, kuma 'yan wasan fasaha na kasar za su nuna wasanni a yayin bikin bude taron. Hazalika kuma za'a shirya wani dandali game da muhimmin tarihin birnin Niamey. A cewar ministan matasa, al'adu da wasannin motsa jikin kasar Kounou Hassane dake bada bayani, " Niamey, hedkwatar al'adun musulunci " wannan shiri ne dake cikin tsarin manyan biranen al'adun musulumci, dake da manufar karfafa hadin kai tsakanin kasashen musulumci, tare da taimakon kungiyar ISESCO. Zaben birnin Niamey ya biyo bayan taron ministocin al'adu na kasashen musulumci karo na uku da ya gudana a birnin Doha na kasar Qatar daga ranar 29 zuwa 31 ga watan Disamban shekarar 2011. (Mamana Ada)