A gun bikin bude taron, mataimakin shugaban kungiyar raya cinikin al'ummar kasar Sin Lan Jun ya ce, an kaddamar da bikin ne da zummar sa kaimi ga sana'ar da ta shafi musulmai, kara yin hadin kai tsakanin kasar Sin da sauran kasashen musulmai da habaka hadin kai tsakaninta da sauran kasashe, da kuma samar da wani dandalin tattaunawa kan batun sana'ar da ta shafi musulmai a duniya.
Shugaban kungiyar addinin musulunci na kasar Sin babban liman Chen Guangyuan ya ce, a 'yan shekarun nan, kamfanonin musulmai na samun ci gaba mai kyau wadanda suka taka rawa wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin al'umma.
A nan kasar Sin, kabilu fiye da 10 ciki har da Hui, Uighur, Kazak da sauransu mabiya addinin musulunci ne kuma yawansu ya kai miliyan 23.(Amina)