Taron da aka shirya a wannan rana, an gabatar da ayyukan kungiyar musulmi kula da harkokin musulunci za ta yi a cikin shekaru 5 masu zuwa, Mahalartar taron sun nuna cewar ya kamata a ba da gudumawa a fannonin kiyaye zaman jituwa a tsakanin mabiyar addinai, da hadin kan kabilun kasar Sin, da tabbatar da zaman lafiyar al'ummar kasar, da kuma sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin kasar.
An kafa kungiyar kula da musulunci ta kasar Sin a shekarar 1953, kuma ita ce kungiyar kula da musulunci ta farko a tarihin kasar.(Abubakar)