in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kawo karshen matakin farko na babban taron duniya na addinin Musulunci a Bangladesh
2013-01-14 15:43:56 cri

Ran 13 ga wata da yamma, an kawo karshen babban taron hajin shekara-shekara na addinin Musulunci da ya shafe kwanaki uku a babban birnin kasar Bangladesh, Dhaka, taron da ya kasance matakin farko na babban taron duniya na addinin Musulunci. Miliyoyin masu aikin haji daga kasashen India, Amurka, Australia, Japan da dai sauran kasashe fiye da 100 suka halarci wannan zaman taro na birnin Dhaka. Inda suka gudanar da addu'o'i domin Allah ya kawo zaman lafiya da wadatuwa da zaman jituwa ga dan Adam a duk duniya baki daya.

Tun daga shekarar 2011, aka raba babban taron duniya na masu bin addinin Musulunci zuwa matakai biyu domin kaucewa tashin hankali da hadarin cunkoso da ake samu a lokacin aikin haji.

Shugaban kasar Bangladesh Zillur Rahman, da firaministan kasar Sheikh Hasina, da shugaban jam'iyyar adawa kuma tsohon firaministan kasar Khaleda Zia da dai sauran shugabanni da manyan jami'an kasar za su halarci bikin addu'a da za a gudanar bisa mataki na biyu na wannan babban taron duniya na addinin Musulunci. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China