in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Malaman addinin Musulunci sun bukaci da a saki mutanen da aka yi garkuwa dasu a yankin Sahel na nahiyar Afrika
2012-11-03 17:38:16 cri
Malaman addinin Musulunci wadanda suka gana a Makka lokacin aikin haji da aka kamala kwanannan sun yi kira ga wadanda suka yi garkuwa da mutane da su nuna adalci tare da sakin mutanen da suka yi garkuwa dasu a yankin Sahel na nahiyar Afrika.

A wata sanarwar da kamfanin dillancin labarai na kasar sin Xinhua ta samo a jiya juma'a,malaman addinin daga kasashen Aljeriya, Mauritaniya,Niger da kuma Nigeriya wadanda suka gana a birnin Makka sun yi kira ga shugabannin wadannan kungiyoyi masu dauke da makamai musamman AQIM,MUJAO da Boko Haram da suka sake nazari a kan akidar su kuma su aje makaman su.

Sun bukaci wadannan kungiyoyi da su saki bayin Allah da basu ci ba basu sha ba da suke garkuwa dasu ko da musulmai ne ko baki 'yan kasashen waje.

Malaman addinin na Musulunci sun yi shawaran saka baki ne ganin yadda sha'anin jin kai da tsaro yake kara tabarbarewa a gabar kudancin hamadan Sahara.Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare ana fakewa da wai ana jihadin na daukaka addini,inji sanarwar Malaman.

Sanarwar ta kara da cewa " Ganin yadda aka jahilci addini.masu aikata laifukan suna sace har da musulmai da fararen hula 'yan kasashen waje,abinda ya saba ma koyarwar addinin Musulunci game da hakuri,zaman lafiya da zamantakewar walwala da kwanciyar hankali tsakanin mabiya addinai daban daban.

A cikin rokon,wanda malaman suka kawo misalai daga ayoyin Qur'ani,Jagoran Musalmai na kasar Mauritaniya Sidi Mohammed Ould Showef yayi tir da yadda ake fakewa da addini ana garkuwa da mutane,a cewar sa wadannan dabi'u ya kawo rashin tsaro a yankunan musulmai kuma yana bada kafa ga makiya addinin musulunci da suke amfani da irin wadannan misalai domin raba kan musulmai.

Malaman addinin Musuluncin na Aljeriya,Nigeriya,Niger da Mauritaniya sun kuma bukaci shugabannin wadannan kungiyoyi masu dauke da makamai a arewacin Mali su kawo karshen zub da jini na 'yan uwansu musulmai da suke yi. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China