Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya (NEMA) ta bayyana cewa, wata gobara mai ban al'ajabi ta tashi a wani ofishin hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya da ke unguwar Maitama a birnin Abuja, amma ba wanda ya jikkata ko ya mutu.
Mai magana da yawun hukumar Yusha'u Shu'aib ya ce, gobarar ta shafi ne a ofishin darektan hukumar mai kula da adana muhimman takardu, kuma nan da nan jami'an hukumar kashe gobara ta kasa suka shawo kanta, sai dai har yanzu ba a san musabbin gobarar ba.
Bugu da kari, wata tawagar 'yan sandan kwantar da tarzoma da kuma 'yan sandan yau da kullum suka yi wa wurin kawamya a matsayin wani matakin mayar da martanin gaggawa don ganin an kashe wutar.
Jami'in na NEMA ya ce, matakin gaggawa da 'yan kwana-kwanan suka dauka, ya taimaka wajen hana wutar ta haddasa wata barna tare da bazuwa zuwa sauran ofisoshin da ke harabar hedkwatar.
Wata majiya ta ce, ana fargabar cewa, wasu fayil-fayil masu muhimman takardu na iya bacewa sanadiyar gobarar, sannan gobarar ta lalata ofishin da wutar da tashi a ciki.(Ibrahim)