in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sakamakon gobara a arewa maso gabashin Sin ya haura zuwa 120
2013-06-04 10:01:07 cri

Hedkwatar aikin ceto ta bayyana cewa, adadin mutane da suka mutu sakamakon gobara a wata ma'aikatar dabbobi dake jihar Jilin a arewa maso gabashin kasar Sin ya haura zuwa 120, da karfe 8 na daren ranar Litinin, yayin da wasu 70 suka samu rauni.

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe shida da mintoci shida na safe a wata ma'aikatar sarrafa dabbobi, mallakar kamfanin dabbobi ta Jilin Baoyuanfeng, a Mishazi dake cikin garin Dehui mai nisan kilomita 100 daga birnin Changchun, hedkwatar jihar.

An kafa wata tawagar bincike ta kasa ranar Litinin, karkashin jagorancin shugaban sashen tabbatar da kiyaye lafiya a wajen aiki, Yang Dongliang, domin gudanar da cikakken bincike dangane da musabbabin gobarar. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China