Hafsan hafsoshin sojojin Jamhuriyar Kasar Kwadibwa Soumaïla Bakayoko ya bayyana wa 'yan jarida cewa, sojoji guda 600 sun fara tashi zuwa yankin yammacin kasar tun daga ranar 1 ga wata, kuma mafi yawansu sun je jihar Toulepleu da sauran jihohi 2 dake makwabtaka da kasar Liberia.
Ya ce, wadannan sojoji za su fara aikin kiyaye zaman lafiya a kan iyakar kasar dake yankin yamma tun daga ranar 6 ga wata, don tabbatar da gudanar da zaben birane da garuruwa a yankin yadda ya kamata. (Zainab)