in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya amince da sabunta aikin hukumar MDD a Kwadibwa da shekara daya
2013-07-31 10:23:44 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya tsayar da kuduri a ranar Talatar nan 30 ga wata na sabunta aikin hukumar MDD a kasar Kwadibwa (UNOCI) na tsawon shekara daya.

A cikin kudurin, kwamitin ya kara yawan lokacin aikin har zuwa watan Yunin shekarar 2014, kana ya jadadda bukatar ganin gwamnatin kasar ta Afirka tana inganta zamantakewar lumana da samar da kariya bai daya ga dukkan farar hula.

Kudurin na mai nuna cewar aiki da hukumar ta MDD ta UNOCI ta sa gaba shi ne samar da kariya ba tare da wata hassada ba ga mahukuntan kasar Kwadibwa, da kuma kare farar hula daga dukkan wata barazana mai illa, da iya karfin da take da shi, a wurare da take aiki.

Kwamitin sulhu har wa yau ya bukaci UNOCI da ta mai da hankali kan kawar da dukkan sauran barazana dake akwai a fuskar tsaro da kalubale dake da nasaba da kan iyaka.(Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China