in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kwadibwa zai shiga babban zaben da za a yi a shekarar 2015
2013-07-04 10:55:15 cri
Ran 3 ga wata, shugaban kasar Kwadibwa Alassane Ouattara ya ba da sanarwa a hukunce, inda ya nuna cewa, zai shiga babban zaben da za a yi a shekarar 2015, don ci gaba da shugabancin kasar da kuma ba da gudumawa wajen gudanar da ayyukan gina kasa cikin zaman lafiya.

A wannan rana, shugaba Alassane Ouattara ya kai ziyara a garin Mbengue da ke arewacin kasar, yayin da a taron jama'a ya bayyana cewa, ya riga ya yanke shawara kan shiga babban zaben shugaban kasa da za a yi don neman wa'adin aikinsa na zagaye na biyu, don ci gaba da aikin shimfida zaman lafiya a duk fadin kasar Kwadibwa. Bugu da kari, ya yabi gwamnatin kasar ta yanzu domin kokarin da ta yi wajen gina kasa, ta yadda aka samu kwanciyar hankali a duk fadin kasa, kuma a halin yanzu, ana lokacin farfadowar kasa.

Bayan an kammala babban zaben shugaban kasar Kwadibwa a watan Nuwamba na shekarar 2010, shugaban wancan lokaci Laurent Gbagbo da kuma shugaban jam'iyyar adawa Alassane Ouattara dukkansu sun sanar da cimma nasarar zaben, da kuma rantsar da kansu kan matsayin shugaban kasa, abin da ya haifar da fadace-fadace a tsakanin magoya bayan bangarorin biyu. Daga bisani kuma, an kama Laurent Gbagbo a watan Afrilu na shekarar 2011, sannan aka rantsar da Alassane Ouattara a matsayin shugaban kasa, aka kafa sabuwar gwamnatin kasa, sai dai rayukan mutane a kalla dubu 3 suka salwanta a sanadiyyar wannan takaddama wadda ta dauki tsawon watanni biyar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China