in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya yi kira ga shugabannin kasashen Afirka da su yi kokarin tabbatar da kwanciyar hankali a fuskar siyasa
2013-03-02 16:35:41 cri
Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan, wanda ya kai ziyara kasar Kwadibwa a ranar Jumma'a 1 ga wata, a birnin Yamousoukro ya ce zai ci gaba da nuna azama tare da takwaransa na Kwadibwa Alassane Dramane Ouattara, da ma sauran shugabannin kasashe membobin kungiyar ECOWAS a kokarin tattabar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da samun habakar tattalin arziki a wannan yanki.

A yayin da yake jawabi a babban zauren taro dake birnin Yamousoukro, Jonathan ya ce, kamata ya yi shugabannin kasashen Afirka su yi kokari tare, domin samar da wani yanayin siyasa na kwanciyar hankali a kasashensu, da ma a nahiyar Afirka baki daya, ta yadda zai kai ga haifar da habbakar tattalin arziki.

Jonathan ya kara da cewa, kwanciyar hankalin siyasa da ci gaban tattalin arziki na da wata alaka ta kut da kut, don haka idan ba'a samu kwanciyar hankali a kasa ba, tattalin arzikin kasar ba zai bunkasa ba, kuma idan tattalin arzikin kasa ya habaka, zai taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali.

Har wa yau, shugaba Goodluck Jonathan ya jaddada cewa, kungiyar ECOWAS ba za ta samu damar taka rawar gani a harkokin duniya ba, sai in kasashen dake wannan yanki sun yi kokarin raya tattalin arzikinsu da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen nasu. (Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China