in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Kwadibwa sun yi bikin cika shekaru talatin da kulla huldar diplomasiyya
2013-03-02 16:00:37 cri
A ranar Asabar din nan ne Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi musayar sakonnin fatan alheri da takwaransa na kasar Kwadibwa Alassane Ouattarra dangane da bukin cika shekaru talatin da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Hu ya bayyana cewa cikin mutunta juna da adalci, ana samun ci gaban kyakkyawan hulda da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Kwadibwa tun daga lokacin da suka kulla abuta ta diplomasiyya.

Bangarorin biyu suna baiwa juna goyon baya kan batutuwan da suke da muhimmanci, kana suna kyautata hadin gwiwa kan batutuwa na kasa da kasa da ma na yanki. Hu ya ci gaba da cewa aminci ta siyasa tsakanin kasashen biyu ya ci gaba da bunkasuwa,

Yace kasar Sin tana amfani da wannan lokaci na cika shekaru talatin da kulla dagantakar wajen kara yaukaka kawance da hadin gwiwa da Kwadibwa don moriyar jama'ar kasashen biyu.

A cikin nasa sakon, Ouattara ya ce, Kwadibwa tana mai gamsuwa kan hadin gwiwa tsakaninsu tare kuma da nuna imanin cewa akwai kyakkyawar makoma dangane da kawance da kasashen biyu suka kulla.

Kasar Sin ta jima tana ba da goyon baya ga kasar Kwadibwa a fuskar zaman lafiya da bunkasar kasa, kana shugaban na Sin ya ce kasar a shirye take wajen ganin cewa an samu karin ci gaban hulda tsakanin kasashen biyu. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China