A cewar sojojin kasar Siriya, kai yaki a Al-Khalidieh muhimmin aiki ne, bisa dalilin matsayin da wannan wuri yake da shi kuma zai canja salon yaki a birnin Homs bisa moriyar sojojin kasar.
Haka kuma sanarwar ta kara nuna cewa, sojojin kasar na cigaba da ayyukansu cikin nasara domin kawar da duk wasu ayyukan ta'addanci daga fadin kasar Siriya.
Rundunar sojojin kasar ta Siriya, ta dauki niyyar kai babban samame a makon da ya gabata a wannan sansani na 'yan tawaye dake tsakiyar Homs, bayan sojojin na Siriya sun karbe garin Qoussair dake kan iyaka da kasar Lebanon a watan da ya gabata.
MDD ta fitar da wasu alkaluma dake bayyana cewa mutane fiye da dubu dari aka kashe a cikin wannan rikici na kasar Siriya, watanni ashirin da takwas tun bayan barkewarsa, a yayin da mutane miliyan 1.7 suka yi gudun hijira zuwa kasashen dake makwabtaka da kasar Siriya. (Maman Ada)