in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi musayar wuta a tsakanin masu adawa da gwamnatin Syria
2013-07-14 17:02:34 cri
A ranar 13 ga wata, hukumar binciken hakkin dan Adam ta kasar Syria ta bayyana cewa, dakarun kungiyar adawa ta kasar Syria ko sojojin 'yantar da kasar Syria sun yi musanyar wuta da dakarun wata kungiyar adawa ta daban a arewacin kasar.

Bisa sanarwar da wannan hukuma ta bayar a ranar 13 ga wata, an ce, membobin kungiyoyin biyu sun yi dauki-ba-dadi a wani kauyen dake arewacin kasar ta Syria. Amma wannan sanarwa ba ta bayyana yawan mutanen da suka mutu ko suka jikka ba. Manazarta sun yi amannar cewa, barkewar rikici a tsakanin kungiyoyin masu adawa da gwamnatin kasar ta Syria zai kara rage karfinsu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China