A ranar Talata ne asusun kula da harkokin yara na MDD, UNICEF ya bayyana cewa, rikicin da ake yi a kasar Syria na da barazanar haifar da mummunan sakamako ga rayuwar yara, har iya kawo barazana ga tsawon rayuwarsu.
Rahoton da asusun ya samar ranar Talatar nan, na mai dora laifin wannan barazana kan tashin hankali da yakin karewa, rasa muhalli na dimbin jama'a, da kuma lalacewar ababan more rayuwa da sauran muhimman hidimar yau da kullum.
A cikin rahoton, UNICEF na mai nuni cewar, yara a kalla miliyan biyu ne da rikicin na kasar Syria ya shafa.
Rahoton ya yi tsokacin cewa, a cikin tsawon shekaru 2 da aka shafe ana wannan rikici, musamman ma a wurare da rikicin ya fi tsananta, ana fuskantar matsalar ruwan sha wadda ta haifar da cututtuka da suka shafi fatar jiki da numfashi.
A halin da ake ciki kuma, an lalata kashi daya bisa biyar na makarantun Syria, kana ana amfani da wasunsu a matsayin matsugunan iyalai da suka rasa muhallinsu, in ji rahoton, ga kuma halin firgita da wasu yaran suka shiga sakamakon ganin yadda aka kashe 'yan uwa ko abokansu a idansu, baya ga barazana da suke yi da kara da kuma abin da idanunsu ke gane masu na rikicin, wanda ya barke tun cikin watan Maris na shekarar 2011 sakamakon matsalar ta siyasa.(Lami)