in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukuma mai kula da hakkin bil Adama ta zartas da kuduri kan batun Syria
2013-06-15 16:55:45 cri
A ranar Jumma'a 14 ga wata, a wajen zama na 23 na hukuma mai kula da hakkin bil Adama ta MDD wanda ya gudana a birnin Geneva dake kasar Switherland, an zartas da wani daftarin kuduri kan yanayin da ake ciki a kasar Syria a fannin hakkin bil Adama.

A cikin kudurin, an yi Allah wadai da ayyukan keta hakkin dan Adam da bangarorin kasar dake rikici da juna suke aikatawa, haka kuma ana karawa gwamnatin kasar Syria matsin lamba, don ganin ta hada kai da kwamitin kasa da kasa na binciken yanayin da ake ciki a kasar Syria.

Har ila yau, fadar shugabancin kasar Faransa ta sanar a ranar 14 ga wata cewa, don share fagen taron kolin kungiyar G8 da za a kira, shugaban kasar Faransa Francois Hollande, da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama, da shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel, da firaministan kasar Birtaniya David Cameron, da kuma firaministan kasar Italiya Enrico Letta, sun kira taro ta telabijin da wayar tarho, inda suka tattauna batun Syria.

A nasa bangare, wani jami'i mai taimakawa shugaban kasar Amurka a bangaren kulawa da aikin tsaron kasa Ben Rhodes, ya furta ran Alhamis 13 ga wata cewa, kasar Amurka ta tabbatar da cewa sojojin kasar Syria sun yi amfani da makamai masu guba don yaki da dakarun 'yan adawa, lamarin da suke ganin ya wuce abin da za a iya hakura, don haka shugaba Obama ya yanke shawarar ba da tallafi a fannin aikin soja ga 'yan adawa na kasar Syria kai tsaye.

Daga bisani kuma, babban magatakardan MDD Mista Ban Ki-moon, ya nuna kin amincewarsa kan niyyar da kasar Amurka ta dauka na samar da makamai ga 'yan adawan kasar Syria. Cikin sanarwar da ya yi a ranar 14 ga wata, Mista Ban Ki-moon ya ce matakin ba zai taimakawa kokarin sassanta yanayin da kasar Syria ke ciki ba.

A cewar Mista Ban, matakan soja ba za su daidaita rikicin Syria ba, maimakon haka za su kara haddasa wargajewar al'ummar kasar, tashin hankali a yankuna daban daban, da samun karin kiyayya a tsakanin addinai da al'ummomi daban daban. Don haka, ya nanata cewa, samar da karin makamai ga duk wani bangaren kasar zai tsananta yanayin da ake ciki.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China