A gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana, Del Buey ya bayyana cewa, wakilin musamman na MDD da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa kan batun Syria Lakhdar Brahimi zai jagoranci tawagar wakilan MDD don halartar shawarwarin.
Kana Del Buey ya nuna damuwa ga halin rayuwa da kananan yara na kasar Syria ke ciki.
A ranar 11 ga watan Janairu na bana, Brahimi ya taba yin shawarwari tare da mataimakin ministan harkokin waje na kasar Rasha Mikhail Bogdanov da mataimakin sakataren harkokin waje na kasar Amurka William Burns a birnin Geneva don tattauna shirin warware rikicin kasar Syria ta hanyar siyasa, amma bangarorin uku ba su cimma daidaito ba. A farkon watan Mayu na bana, sakataren harkokin waje na kasar Amurka John Kerry ya kai ziyara a kasar Rasha, inda shi da ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergei Lavrov suka bada shawarar gudanar da taron kasa da kasa kan batun Syria karo na biyu. (Zainab)