Kerry ya bayyana hakan ne yayin ganawa da 'yan jarida, bayan wata ganawa da yayi da magatakardan MDD Ban Ki-Moon.
Ya ce sun dage kan kokarin hada bangarorin biyu kan tebur tattaunawa a karo na biyu a Geneva, domin a aiwatar da matakai da aka cimma a taron Geneva na farko, kuma zasu ci gaba da kokarin ganin an cimma nasara nan ba da dadewa ba.
A nasa bangare, Ban yace wajibi ne bangarorin su daina daukar duk wani mataki na soji da fadace –fadace kuma ya zama dole a yi zaman tattauanawa a Geneva game da shimfida zaman lafiya a Syria, nan ba da dadewa ba, kamar yadda Mr Kerry da Mr Lavrov suke bada shawara, inda ya kara da cewa shi da wakilin musamman na AU da MDD kan batun na Syria, Lakhdar Brahimi, za su yi kokarin tabbatar da kiran wannan zaman ganawa ba tare da bata lokaci ba. (Lami)