Bayan kammala taron wanda aka gudanar cikin 'yan awoyi, an kuma gabatar da gajeriyar sanarwar dake bayyana cewa, kasashe mambobin kungiyar abokan Sham, suna da ikon zabar hanyar da ta fi dacewa, domin taimakawa jam'iyyu masu adawa da gwamnatin kasar ta Sham, haka kuma za su sauke dukkanin nauyin dake wuyansu, na kalubalantar mahukuntan Sham, domin hana su nuna karfin tuwo kan 'yan adawa, a kokarin daidaita matsaloli a siyasance, bisa kuma sanarwar taron Geneva da kuma sauran dokoki masu alaka da hakan. Wakilai daga kasashe biyu ne kacal suka nuna rashin amincewa da ba da taimakon aikin soja ga jam'iyyun adawa da gwamnatin ta Sham.
Bayan taron, ministan harkokin waje na Qatar, Hamad Bin Jassim Bin Jabor Al-Thani, ya kira taron manema labaru tare da takwaransa na Amurka, John Kerry, inda ya furta cewa, dukkan kokarin kasashen Larabawa, da na sauran kasashen duniya ya ci tura. Bai kuma kamata kasashen duniya su ci gaba da jira ba, musamman ma gani cewa kwamitin sulhu na MDD kawo wannan lokaci bai cimma matsaya guda kan batun Sham ba, a maimakon haka, dole ne a dauki matakai cikin sauri, domin kawo karshen wannan matsala ta kasar Sham.
A nasa bangare, sakataren harkokin waje na Amurka, John Kerry ya nuna amincewa da hana sake abkuwar hare-hare na nuna fin karfi a kasar ta Sham, ya kuma ce ya amince da baiwa jama'ar kasar damar yanke shawara da kansu, a sa'i daya, bai kamata a taimaki kowane bangare domin samun moriya ko yin nasara a bangarorin biyu ba. Ya ce, makasudin nuna goyon baya ga jam'iyyun adawa da gwamnatin kasar ta Sham shi ne, kiyaye moriyar jama'ar kasar da kuma samar musu da makoma mai kyau. Ya kara da cewa, mahukuntan kasar da kuma 'yan adawa, suna iya gabatar da dan takarar jagorancin kasar na nan gaba, wanda zai iya kiyaye iko da moriyar jama'ar kasar baki daya, a kokarin da ake yi na daidaita batun kasar cikin lumana.(Fatima)