A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, hukumar kulawa da shiga tsakani game da rikicin kasar Mali ta kungiyar ECOWAS ta bayyana cewa, bayan da wakilan ECOWAS, na kasar Mali da na dakarun Tuareg wato NMLA suka yi shawarwari game da batun kasar Mali, sun cimma matsaya kan wannan batu.
Hukumar kula da shiga tsakani ta kungiyar ECOWAS ta ce, nan ba da dadewa ba, gwamnatin wucin gadi ta Mali da dakarun adawar kasar za su yi shawarwari kai tsaye a tsakaninsu a karkashin jagorancinta, don sa kaimi ga gudanar da babban zaben kasar da wuri.
Shugaban gwamnatin wucin gadi ta kasar Traore ya bayyana cewa, shi kansa da sauran mambobin majalisar dokoki ta gwamnatin wucin gadi, ba za su shiga babban zaben bisa matsayin 'yan takara ba.(Bako)