Za a gudanar da zaben shugaban kasar Mali a ran 28 ga wannan wata da muke ciki. A ran 7 ga wata aka fara yakin neman zaben. Ko da yake gwamnatin kasar Mali da kasashen duniya sun yi imanin kan cewa za a gudanar da zaben cikin lokacin da aka kayyade, amma akwai ayar tambaya kan wannan batu saboda ganin cewa babu cikakken zaman karko a arewacin kasar, kuma sharadin yin zabe bai samu dacewa ba.
'Yan takara guda 36 ne suka sanar da shiga zaben a wannan karo, to amma kotun tsarin mulkin kasar ta dakatar da mutane 8 daga cikinsu bisa dalilin tattalin arziki, tawagarsu da sauransu, inda yanzu 'yan takara 28 ne suka rage ciki hadda tsoffin shugabannin kasar 4.
Har wa yau, shugaban rikon kwaryan kasar Dioncounda Traore ya yi jawabi a daren ran 6 ga wata inda ya yi kira ga jama'a da su goyi bayan zaben da za a yi. Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Mamadu ya bayyana a wannan rana cewa, yana fatan 'yan takarar zasu yi takara yadda ya kamata bisa doka, tare kuma da bayyana kan na hadin gwiwar al'umma da kishin kasa.
A ran 7 ga wata, 'yan takarar da suka fito daga manyan jam'iyyu da kungiyoyin kasar sun yi taruruka a wurare daban-daban domin samun goyon bayan jama'a. Juyin mulkin da aka yi a watan Maris na shekarar bara, ya haifar da baraka a kasar, tare da koma bayan tattalin arziki da rashin aikin yi. Don haka, 'yan takara da dama sun yi alkawari kan wasu abubuwa, ciki hadda zaman lafiya, tsaro, ba da ilmi, samar da guraben aikin yi da bunkasa tattalin arziki da sauransu.
To amma fa 'yan takara ba su yi yakin neman zabe a yankuna da masu fafutuka suka mamaye ba. Ko da yake, gwammati da masu fafutuka a arewacin kasar sun kulla yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a watan da ya gabata, amma mutane Tuareg dake yankin Kidal suna ci gaba da gwabzawa, inda su kan yi zanga-zanga da daukar matakan takalar rundunar kiyaye zaman lafiya da sojojin gwamnatin kasar dake girke a wurin.
Wani jami'in hukumar tsaron kasar ya ce, masu fafutuka a yankin Kidal su kan yi fito-na-fito da rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD, sojojin kasar Faransa da sojojin gwamnatin kasar Mali, kuma ya yiwu za su tada zaune tsaye kafin a fara babban zabe.
Ban da haka, babu tabbaci ko dubban 'yan kasar Mali da suke gudun hijira a kasashen waje za su iya kada kuri'u yadda ya kamata ko a'a. Kuma rashin samar da kuri'u cikin lokaci zai iya kawo cikas ga zaben. Wani mai zabe ya shedawa manema labaru cewa, ya sami kuri'a, amma har yanzu babu zabukan kada kuri'a a birnin Bamako hedkwatar kasar.
Kasashen duniya na ba da taimako ga gwamnatin kasar Mali domin mawuyacin hali da ake fuskanta yanzu. MDD ta kaddamar da aikinta na kiyaye zaman lafiya a kasar Mali daga ran 1 ga wata domin ta maye gurbin sojojin kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS, da nufin tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabe da ma a arewacin kasar. An ce, a ran 5 ga wata, sojojin kasar Mali sun shiga yankin Kidal, inda gwamnati ta sanar da kawo karshen dokar ta baci da aka kafa a wurin a rabin shekara da ta gabata.
A ran 6 ga wata kuwa, masu sa ido kan babban zaben kasar na EU sun isa kasar, kuma za su sa ido ne kan yadda za a yi zabe a kudancin kasar. Bangarori daban-daban na fatan wadannan kokarin da ake yi za su taimakawa kasar Mali wajen gudanar da zabe yadda ya kamata. (Amina)