in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cibiyar MDD za ta taimakawa 'yan gudun hijiran kasar Mali domin su shiga zaben shugaban kasa dake tafe
2013-06-29 16:25:00 cri
Kasancewa sauran wata guda a gudanar da zaben shugaban kasar Mali, Eduardo Del Buey, mataimakin mai magana da yawun sakatare janar na MDD yayin ganawa da 'yan jarida da aka saba yi kullum yace, ofishin hukumar kula da 'yan gudun hijra ta MDD (UNHCR) ta bayyana ranar Jumma'a cewa, tana kara himma a kan ayyukanta a fuskar taimakawa kasashe makwabtan kasar Mali, a aikin taimakwa 'yan gudun hijira su jefa kuri'a, kafin 28 ga watan Yuli, wato ranar zaben shugaban kasar Mali.

A fadinsa, kasashen Burkina Faso, Nijar da Mauritaniya baki daya suna da 'yan gudun hijira dubu 175 da suka gudu daga kasar Mali sakamakon rikicin baya bayan nan.

Del Buey ya ci gaba da cewa hukumar kula da 'yan gudun hijiran na taimakawa wajen ganin 'yan gudun hijiran sun shiga zaben, duk da cewa ayyukanta na jin kan bil Adama ne ba na siyasa ba.

Ya lura cewa hukumar tana samar da muhimman bayyana ga 'yan gudun hijran dangane da 'yancinsu na shiga zaben kana tana samar masu ababan sufuri.

Wannan zabe yana da muhimmanci ga maido da martabar kasar Mali da kuma mulki bisa tsarin dokoki bayan juyin mulkin soja da aka yi ran 22 ga watan Maris na shekarar 2012, wanda kuma ya haifar da shigowa da mamayar 'yan tawaye dake da alaka da kungiyar Al-Qaida a arewacin kasar Mali na tsawon watanni.

Bisa goyon bayan tsohuwar gwamnatin mulkin mallaka a kasar wato Faransa da sauran kasashen yankin, an samu nasarar fatattakar 'yan tawayen daga muhimman birane a arewacin kasar Mali tun watan Janairu inda aka samu dawo da ikon gwamnati a yankin arewacin kasar da ya yi fama da rikici.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD a lokutan baya ta taimakawa 'yan gudun hijiran kasar Sudan ta Kudu su jefa kuri'a a shekarar 2011, a kasar Iraki a shekarar 2010 da kuma Afganistan a shekarar 2004, inji del Buey.(Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China