in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
PNUD na horar da kungiyoyin fararen hula domin sanya ido kan kare 'yancin dan adam a lokacin zaben shugaban kasa a kasar Mali
2013-07-23 15:21:57 cri
Ministan shari'an kasar Mali Malick Coulbaly ta bakin wakilinsa Djibril Kane ya jagoranci bikin bude taron kara wa juna ilimi a ranar Litinin a Bamako da tsarin cigaba na majalisar dunkin duniya (PNUD) ya shirya game da sanya ido kan kare hakkin dan adam lokacin zabe. Makasudin wannan dandali na kara wa juna ilimi shi ne na samar da makaman aiki ga mahalarta taron maza da mata dabaru da kwarewa kan sanya ido game da kare 'yancin dan adam a kafin lokacin zaben shugaban kasa da kuma bayan lokacin zaben shugaban kasa domin samun damar tattara bayanai kan wasu ayyukan keta hakkin dan adam ta yadda za'a daidaita wannan matsala.

Mista Guillaume N'Gefa, shugaban reshen kare hakkin dan adam na tawagar tabbatar da zaman lafiya na MDD a kasar Mali (MINUSMA) da ya halarci bikin bude wannan taro a cikin jawabinsa ya bayyana cewa girmama 'yancin dan adam abu ne mai matukar muhimmanci wajen kafa wani yanayin zabe cikin 'yanci ba tare da barazana ba. Haka kuma ya kara da cewa idan ba'a girmama hakkin dan adam a lokacin zabe ba, to dole ne sakamakon zabe ya kasance tushen gardama da rikici. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China