in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kare makon farko na yakin neman zabe a Mali lami lafiya
2013-07-16 11:12:16 cri

An kare makon farko na yakin neman zaben shugaban kasa zagaye na farko a ranar lahadi da ta wuce lami lafiya a kasar Mali, wanda za'ayi ranar 28 ga watan Yuli.

Zagayen farko na kamfen da aka fara ranar 7 ga watan Yuli, an kare ba tare da wata matsala ba a kasar dake yammacin Afirka.

An lika hotunan 'yan takara kusa da juna a manyan tituna musamman ma a babban birnin kasar Bamako.

Kwana daya kafin fara kamfen, shugaban hukumar zabe na kasar (CENI) Mamadou Diamoutai ya yi wa 'yan takara tuni kan sassa na 72 da 73 na dokar zaben kasar Mali.

Sashe na 73 na dokar zaben ya hana duk wani dan takara yin amfani da munanan kalamai ko batanci kan abokin hamayarsa.

Wani muhimmin abu har wa yau dangane da zaben shi ne ci gaba da aka samu kan batun karbar katin shaidar dan kasa (NINA) a makon farko.

Alkalumma sun nuna cewar ya zuwa ranar 14 ga watan Yuli, an karbi a kalla kashi 60 cikin dari a fadin kasar.

Mahukuntan kasar sun yi nunin cewa za'a ci gaba da karbar rajistar zabe har zuwa 27 ga watan Yuli. (Lami Ali Mohammed)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China