Majalisar zartarwas ta gwamnatin a lokacin wani zama na musamman da ta yi ta amince da dokar da ya tsaida ranar 28 ga watan Yuli a matsayin ranar zaben shugaban kasar.
Wata sanarwar da aka fitar bayan wannan ganawa ta musamman da Shugaban kasar Malin Diacounda Traore ya jagoranta ya ce, bisa ga doka mai lamba 2013-478/P/RM na ranar 27 ga watan Mayu na wannan shekara, ana sa ran masu jefa kuri'a daga ko'ina cikin kasar da kuma ofisoshin jakadancin kasar dake wassu kasashe za su fito a ranar 28 ga watan Yuli domin zaben Shugaban kasa.
Za'a yi zagaye na biyu a ranar 11 ga watan Agusta mai zuwa idan har dukkannin 'yan takarar ba su samu adadin kuri'un da ake fatan samu ba a zagaye na farko.
Yakin neman zabe na zagaye na farko za'a fara shi ne tun daga karfe 12 dare na wayewar garin 7 ga watan Juli kuma a dakatar da shi da karfe 12 dare wayewar garin ranar 26 ga watan yuli, in ji sanarwar.
Idan har bukatar zaben raba gardama ya kama za'a sake gudanar da yakin neman zaben kwana daya da sanar da sakamakon zaben zagaye na farko sannan za'a dakatar da yakin neman zaben da karfe 12 na dare wayewar garin ran 9 ga watan Agusta.
Kasar Mali tana sa ran ganin sabuwar zamani bayan wannan zabe. Kasar dake karkashin yammacin Afrika ta fuskanci tashin hankali sosai a ranar 22 ga watan Maris na shekarar bara inda 'yan tawayen arewacin kasar suka yi amfani da damar da suka samu na juyin mulkin da soji suka yi suka karbe wannan yanki, har sai a watan Janairun bana da kasashe abokan Mali da suka hada da kasar Faransa suka taimaka mata ta kwato yankunan ta dake ta gefen hamadarta. (Fatimah Jibril)