A wannan rana, shugaba Elbashir da shugaba Kiir sun halarci taron majalisar kiyaye zaman lafiya da tsaro ta kungiyar AU, daga baya sun yi shawarwari cikin sirri. Bayan da aka yi shawarwarin, shugabannin biyu sun yi musafaha tare da murmushi a yayin wannan ganawa.
Babban wakilin kasar Sudan ta kudu Pagan Amum ya bayyana wa 'yan jarida cewa, an yi shawarwarin cikin yanayi mai kyau, shugabannin kasashen biyu sun amince da bada umurni ga tawagoginsu da su gaggauta yin shawarwari da tsaida kuduri da cimma yarjejeniya a kan manyan batutuwa.
Mr Amum ya bayyana cewa, yanzu shi ne lokacin kawo karshen rikici da cimma yarjejeniya a tsakanin Sudan da Sudan ta kudu. Idan aka cimma yarjejeniya cikin adalci, kasar Sudan za ta yi alkawari ga kasar Sudan ta kudu wato maido da samar da man fetur. (Zainab)