in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fada ya barke kan iyaka tsakanin kasar Sudan da Sudan ta kudu
2012-06-09 16:57:02 cri
Ministan tsaro na kasar Sudan, Abdul-Rahim Mohamed Hussein ya tabbatar da fafatawar da ta gudana tsakanin dakarun kasar Sudan da na kasar Sudan ta kudu a kan iyakar kasashen a ranar Jumma'a, daga bangeren kasar Sudan.

Ministan ya sanar a taron manema labarai da ya gudana a garin Khartoum cewa, fafatawar ta gudana ne a yankunan Al-Meram da na Bahral-arabes wadanda suke kusa da iyakar kasashen biyu, wato Sudan da Sudan ta kudu, da kuma a yankin Darfur na kasar ta Sudan.

Ya sanar da cewa, ba su hida shakku ba ga kasar Sudan ta kudu a game da gudanar da wannan lamari, kamar irin na yankin Heglig, amma kuma a shirye suke a game da hakan. Sai dai kuma, ba mu da wani tunani kan yaki da Sudan ta kudu, kamar yadda ministan ya jaddada.

A ranar 10 ga watan Afrilu, kasar Sudan ta kudu ta mamaye yankin Heglig, wato yankin Sudan ne da ke da dumbin arzikin man fetur. Sai dai kuma kasar Sudan ta sake karbar yankin daga Sudan ta kudu a ranar 20 ga watan na Aprilu. (Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China